Hukumar Hisba ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, sun kai ziyarar girmamawa ga Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo.
Ziyarar wadda ta gudana a yau Asabar, na daga cikin matakan ƙarfafa alaƙa da haɗin gwiwa tsakanin hukumar Hisba da Gwamnatin jihar domin inganta ayyukan hukumar samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
A yayin ziyarar, ɓangarorin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban jihar da kuma yadda za’a ƙara bunƙasa ayyukan hukumar domin amfanin al’umma.
