
Ishaq Sani Dambazau
Yan bindiga sun sace Kolawale Mathew Owoade, wani manomi kuma shugaban makarantar ilimin makiyaya da ke karamar hukumar Itesiwaju a jihar Oyo.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Oyo, Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar TheCable a ranar Litinin.
Ya ce an sace Owoade ne da yammacin ranar Asabar yayin da yake dawowa daga gonarsa da ke Budo Aare.
Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya ce ɗan wanda aka sace, Abiola Owoade, ya bayyana cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalan ne jim kaɗan bayan sace shi ta wayar tarhon mahaifinsa, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 30 domin su sake shi.
Abiola ya ƙara da cewa wata tawagar bincike ta gano babur ɗin mahaifinsa a cikin wani daji da misalin ƙarfe 8:20 na safiyar Lahadi, amma ba’a gano inda yake ba.
Wannan lamarin ya faru ne kwana ɗaya bayan da jami’an tsaro suka kuɓutar da ɗalibai da malamai 44 da aka sace a watan Mayu a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo.
