
Ishaq Sani Dambazau
Wata kotu da ke birnin Landan ta wanke tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga tuhume-tuhumen cin hanci guda shida da ake yi mata.
Diezani, wadda ta yi aiki a matsayin ministar albarkatun man fetur tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015 a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ta fuskanci tuhume-tuhume biyar na karɓar cin hanci da kuma tuhuma guda ɗaya ta haɗa baki wajen aikata cin hanci.
Masu gabatar da ƙara sun zargi tsohuwar ministar mai shekaru 65 da samun rayuwa ta alatu a Landan daga wasu masu ruwa da tsaki a harkar mai da iskar gas, waɗanda ake zargin sun yi hakan ne domin samun kwangiloli masu tsoka a Najeriya.
Sai dai bayan shari’ar da aka gudanar, kotun ba ta same ta da laifi kan dukkan tuhume-tuhumen da ake yi mata ba.
