Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya umarci rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina da ta ƙara matakan tsaro a makarantu domin kare ɗalibai, malamai da cibiyoyin ilimi daga barazanar rashin tsaro.
Mataimakin Sufeto Janar mai kula da harkokin kuɗi da gudanarwa, DIG Sulaiman Abdul, ne ya isar da umarnin yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai jihar Katsina.
DIG Abdul ya ce an umarci rundunar jihar da ta ƙara sintiri a makarantu, ƙarfafa tattara bayanan sirri tare da tabbatar da kasancewar jami’an tsaro a makarantu domin hana ayyukan masu aikata laifuka.
Ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen inganta tsaro da kuma samar da yanayi mai kyau ga koyarwa da koyo a makarantu.
A yayin ziyarar, DIG Abdul ya kai duba zuwa Makarantar ‘Ya’yan ‘Yan Sanda da kuma Kwalejin Fasaha da Kasuwanci ta ‘Yan Mata da ke ƙaramar hukumar Charanchi, inda ya tantance matakan tsaron da ake da su.
Haka kuma ya gana da shugabannin makarantu domin jin ƙalubalen tsaro da suke fuskanta tare da tattauna hanyoyin inganta haɗin gwiwa tsakanin makarantu da hukumomin tsaro.
Ya kuma buƙaci shugabannin makarantu da su tsaurara matakan kula da shiga da fita cikin makarantu tare da kai rahoton duk wani motsi ko lamari mai tayar da hankali ga jami’an tsaro.
DIG Abdul ya jaddada cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da cewa ɗalibai da malamai suna gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali da tsaro.
