Ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC Comrd Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya zargi gwamnatin Kano da sakaci kan matsalar daba.
Zargin da gwamnatin ta sha musantawa inda ta bayyana cewa tana ɗaukar matakai daban-daban domin dakile ayyukan daba da sauran laifukan da ke da alaƙa da su.
Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Explorer, inda ya ce har yanzu matsalar daba na cigaba da barazana ga tsaro da zaman lafiyar al’ummar Kano.
Gwarzo ya ce yaudarar kai ne na cewar idan gwamna ya koma jam’iyyar APC tsaro zai samu.
A makon da ya gabata ne dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da haramta ayyukan daba a faɗin jihar Kano, tare da umartar hukumomin tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar domin dawo da zaman lafiya.
