A yayin da aka cika shekaru uku da kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya a jamhuriyar Nijar, makusantan Muhammad Bazoum sun bayyana yadda sojoji ke ci gaba da tsare hamɓararren shugaban kasar da kuma matarsa ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.
Lauyoyi sun ce tsare Bazoum da matarsa tsawon shekaru uku batare da shari’a ba hakan ya sabawa kundin tsarin Mulki.
Kan wannan ne daya daga cikin masu magana da yawun Bazoum Muhammad Abdulkadir Maidalili,yayi karin bayani kan halin da Bazoum ya ke ciki tare da rashin baiwa shari’a dama tayi aikinta yadda ya kamata.
Mohamed Bazoum, da aka zaba a 2021, yana tsare tare da matarsa Hadiza a wani bangare na fadar shugaban kasa da ke birnin Niamey, tun bayan kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
