Shugaban hukumar kula da Zzrga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kawo sauyi mai girma a fannin Sufurin jihar a cikin shekaru uku da suka gabata.
Injiniya Faisal ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai kan nasarorin da gwamnatin ta samu bayan cikar ta shekaru uku akan mulki.
Faisal ya ce hukumar KAROTA ta samu ci gaba mai yawa sakamakon goyon bayan da gwamnati ke bayarwa, da kuma sauye-sauyen da aka aiwatar da zuba jari domin inganta tsaro akan tituna da tafiyar da harkokin zirga-zirga cikin aminci a fadin jihar.
A cewarsa, gwamnatin ta tarar da ƙalubale da dama a bangaren sufuri, amma ta ɗauki matakan da suka ƙarawa hukumar ƙarfi wajen gudanar da ayyukanta tare da inganta ayyukan da take yi wa al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Faisal na cewa ayyukan sabunta birane da gyaran tituna da gwamnati ke yi, sun taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga, rage cunkoso da kuma bunƙasa harkokin tattalin arziki a cikin birnin Kano da sauran sassan jihar.
