Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Kungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN), sun bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa domin dakile matsalar tsaro da ke kara ta’azzara a wasu sassan kasar nan.
A sakon sabuwar shekarar Musulunci, Sarkin Musulmi ya ce lokaci ya yi da yan Najeriya za su hada kai tare da hukumomin tsaro wajen neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Ya kuma umarci limaman masallatai su rika gudanar da addu’ar Qunutun Nawazil tare da ware sallar Juma’a ta farko a sabuwar shekarar Musulunci domin neman taimakon Allah kan matsalar tsaro.
A gefe guda, Limaman Cocin Katolika sun bayyana cewa yan Najeriya sun gaji da kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran hare-haren ta’addanci.
Sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabanni su kara himma wajen samar da tsaro, tare da bai wa jami’an tsaro kayan aiki da goyon bayan da suke bukata domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
