Ofishin lauyoyi na Bashir Yusuf Tudunwazirchi & Associates ya shigar da koke ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, yana neman a gudanar da cikakken bincike kan rushewar wani gini mai hawa uku da ba a kammala ba a unguwar Gaida, da ke karamar hukumar Kumbotso.
Lauyoyin sun shigar da koken ne a madadin wani, Alhaji Surajo Yusuf, wanda ya ce ya rasa dansa sakamakon rushewar ginin.
A cewar takardar koken, lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Agusta, 2026, lokacin da ginin ya rushe ba zato, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane tare da jikkata wasu.
Lauyoyin sun ce kafin faruwar lamarin, mazauna yankin da makwabta sun sha jan hankalin mamallakin ginin kan wasu matsaloli da ake zargin an lura da su, ciki har da yadda aka tsara ginin da kuma yadda ake gudanar da aikin.
Sun kuma yi zargin cewa an gargadi mamallakin ginin kan yiwuwar rushewar ginin idan ba a dauki matakin gaggawa wajen magance matsalolin da aka gano ba.
Saboda haka, lauyoyin sun bukaci ’yan sanda su gudanar da bincike kan Alhaji Ali Nagarta, musamman kan yadda aka gudanar da aikin ginin, da yadda aka kula da shi, da kuma matakan sa ido da aka dauka yayin aikin.
Daga cikin abubuwan da lauyoyin suka bukaci a gudanar da bincike a kansu akwai musabbabin rushewar ginin, rawar da mutanen da ke da hannu wajen ginin suka taka, da kuma alhakin da ya rataya a kansu wajen gine-gine, kulawa da sa ido.
Sun kuma bukaci a gayyaci tare da yi wa duk mutanen da ke da muhimman bayanai game da ginin da gargadin da ake zargin an yi wa mamallakin tambayoyi.
An aike da Kwafin takardar koke ga ofishin gwamnan Kano da hukumar kare hakkin Dan’adam ta ƙasa da kuma ofishin kwamishinan shari’a na Kano.
Lauyoyin sun ce idan binciken ya tabbatar da cewa akwai mutanen da suka aikata laifin da ya dace da hukunci, ya kamata a dauki matakin shari’a a kansu bisa tanadin doka.
Sun ce daukar matakin gaggawa na da muhimmanci, musamman ganin asarar rayukan da lamarin ya haddasa da kuma bukatar daukar matakan da za su hana sake faruwar irin wannan mummunan lamari.
