Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar da kammala jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin 2026.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta ce an kammala jigilar ne bayan tashin jirgin karshe na kamfanin Max Air daga filin jirgin saman Gusau dauke da maniyyatan jihar Zamfara.
Najeriya ta samu kujeru 50,000 domin aikin Hajjin bana, ciki har da kujeru 9,750 da aka ware wa kamfanonin yawon bude ido masu lasisi, tare da jami’an gudanarwa da sauran ma’aikata.
Hukumar ta ce sama da maniyyata 39,000 daga bangaren gwamnati sun isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji, sai dai wasu sun kasa tafiya sakamakon rasuwa ko rashin lafiya bayan an basu biza.
Shugaban hukumar, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya yabawa hadin kan ma’aikatan hukumar, hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, jami’an tsaro, kamfanonin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki wajen samun nasarar aikin jigilar.
Haka kuma hukumar ta godewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, bisa goyon baya da suka bayar domin tabbatar da lafiyar maniyyatan ƙasar nan.
NAHCON ta kara da cewa shirye-shiryen dawo da alhazai gida zai fara daga ranar 3 ga watan Yunin 2026.
