Gwamnatin Jihar Bauchi ta ɗage dakatarwar da ta sanya kan harkokin kasuwanci a wasu kasuwannin shanu da ke jihar gabanin bikin babbar Sallah mai zuwa.
A baya gwamnatin jihar ta dakatar da ayyukan kasuwanci a wasu kasuwannin shanu da ke kananan hukumomin Alkaleri, Bauchi, Kirfi da Tafawa Balewa saboda matsalolin tsaro.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai baiwa Gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, ya ce Gwamna Bala Mohammed ya amince da ɗage dakatarwar domin baiwa al’umma damar sayen dabbobin layya kafin sallah.
Sanarwar ta ce matakin zai yi aiki na tsawon makonni biyu, yayin da jami’an tsaro tare da shugabannin gargajiya da hukumomin yankuna za su ci gaba da sanya ido domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasuwannin.
