
Wata kotun majistare da ke Bwari a Abuja ta bayar da umarnin kamo ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kumbotso, Hon. Idris Dankawu, bisa zargin damfara da ya kai sama da N77m.
Umarnin ya biyo bayan ƙorafin da kamfanin BAMZ Multi Essential Services ya shigar, inda ake zargin an karɓi kuɗin ne ta hannun hadiminsa, Isma’il Yakubu Abubakar, bisa alƙawarin ba da kwangilar saka fitilun hasken rana da ba a aiwatar ba.
