Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniTennis: Naomi Osaka ta janye daga shiga gasar Australian Open

Tennis: Naomi Osaka ta janye daga shiga gasar Australian Open

Date:

Yar wasan tennis Naomi Osaka, ta sanar da janyewa daga gasar Australian Open ta wannan shekarar, kwanaki Takwas kafin ranar farawa.

 

Osaka, wadda ta lashe gasar a birnin Melbourne a shekarun 2019 da 2021, bata fafata a gasar WTA tin Satumbar 2022.

 

Sai dai babu wani dalili na ficewar Yar wasan Mai shekara 25 Yar kasar Japan .

 

Amma tuni masu shirya gasar suka bawa Yar wasan kasar Ukrain Dayana Yastremska, dama domin ta maye gurbin Osaka.

 

Gasar dai ana saran farawa daga ranar 16 ga Janairun da muke ciki a birnin Melbourne.

 

Ko a watan Mayun 2021, Osaka ta fice daga gasar French Open sakamakon rauni da ta bayyana tana dauke da shi musamman abin da ta kira da ciwon damuwa.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...