Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniRonaldo zai rika karbar Fam Miliyan 177 duk shekara, bayan komawarsa Al...

Ronaldo zai rika karbar Fam Miliyan 177 duk shekara, bayan komawarsa Al Nassr

Date:

Kyatfin din kasar Portugal Kuma tsohon dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo zai rika karbar Fam Miliyan 177 a kungiyar kasar Saudi Arabia wato Al Nassr.

 

Kungiyar ta Al Nassr ce ta sanar da daukar Ronaldo a kwantaragin shekara biyu a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Juma’a.

 

“Muna masu sanar da al’umma cewa a wannan rana, mun kammala cimma yarjejniyar daukar Dan wasa Ronaldo zuwa Al-Nassr, wanda muke fatan daukar Ronaldo zai ciyar da kungiyar mu gaba da Kuma samun nasara,” a cewar kungiyar ta Al-Nassr kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

 

Ronaldo kawo yanzu zai kammala komawa kungiyar ne idan ya Isa birnin Riyadh, domin yi masa gwajin Lafiya a kwanaki masu zuwa, duka domin zama cikakken Dan wasan kungiyar.

 

A baya a wata hira da Jan Jaridar kasar Ingila Piers Morgan, yayi da Ronaldo ya tabbatar da cewa ya cimma yarjejniyar zama Dan wasan wata kungiyar da ke kasar ta Saudi.

 

Kuma yanzu haka bayan komawarsa Al Nassr, Ronaldo zai kasance a kungiyar tare da Dan wasan gaban Kamaru Vincent Aboubakar da Tsohon Mai tsaran raga na Arsenal David Ospina.

 

Al Nassr, Kuma kawo yanzu na tunanin zawarcin tsohon abokin Ronaldo a Real Madrid Sergio Ramos, wanda kungiyar da ke buga gasar Saudi Pro League ke nuna sha’awar sa.

 

Kuma Al-Nassr dai yanzu haka na matakin farko a gasar kasar ta Saudi Arabia bayan nasara a wasa Bakwai cikin wasa 10 da aka fafata a sabuwar kakar wasanni ta bana.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...