Saurari premier Radio
24.2 C
Kano
Monday, September 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniMessi ba shi ne dan wasa da babu kamarshi a duniya ba...

Messi ba shi ne dan wasa da babu kamarshi a duniya ba – Ancelotti

Date:

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Carlo Ancelotti, ya ce bai gamsu Dan wasa Lionel Messi shi ne wanda babu kamarsa a kwallon kafa a duniya ba.

 

Ancelotti ya bayyana haka ne a zantawarsa da Jan jaridu a ranar Alhamis dinnan.

 

A cewarsa akwai Yan wasa da kwallon kafa ba zata manta da su ba, musamman gudunmawar da suka taka.

 

Inda ya bayar da misali da Yan wasa kamar Diego Maradona, Alfredo Di Stefano da kuma Johann Cruyff, wanda ya ce duka sun taka rawa matuka.

 

Ancelotti ya ce “Messi Dan kwallo ne gwarzo a duniya, amma fa ba zance shi ne yafi kowa ba”

 

“Matuka akwai Yan Kwallo masu kyau da nagarta da ha zaka, kamar Maradona, Di Stéfano, Cruyff.. amma bansan waye ya fi wani ba”, a cewar Ancelotti

 

A kwanakin da suka gabata dai Lionel Messi ya jagoranci Argentina lashe gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 da ta gudana a Qatar

Latest stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Sabbin Yan Wasa 12 da Kano Pillars ta dauka

Kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars, wadda ta lashe...