Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniKano Pillars ta zabi Yan wasa 40 don tinkarar kakar badi

Kano Pillars ta zabi Yan wasa 40 don tinkarar kakar badi

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Kano Pillars ta zabi Yan wasa 40 da zasu tin kari kakar wasannin shekarar 2022/2023.

 

Mai magana da yawun kungiyar Rilwanu Idris Malikawa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Ahmad Hamisu Gwale.

 

Yana Mai cewa kungiyar karkashin jagorancin mai horarwa Evans Ogenyi ta kammala tantace daukar yan wasan ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a nan Kano.

 

Malikawa ya ce cikin Yan wasa 18 na daga cikin wadanda suka fafatawa Pillars a kakar wasannin da ta gabata.

 

Sai kuma biyar daga ciki an zabo su ne daga karamar kungiyar ta Kano Pillars, ragowar Yan wasan kuwa an dauke su daga kungiyoyi daban-daban.

 

Haka zalika Mailkawa Garu ya ce duka Yan wasan za su je suyi gwajin Lafiya domin shirin fara Sabuwar kakar wasanni Mai zuwa.

Har ma ya ce duka dan wasan da bai tsallake gwajin Lafiya ba to ba zai samu damar kasancewa cikin kungiyar ba.

Latest stories

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...