Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniQatar 2022:Kwallon da Richarliso ya zura itace kwallo mafi kyau a kofin...

Qatar 2022:Kwallon da Richarliso ya zura itace kwallo mafi kyau a kofin duniya

Date:

Dan wasan kasar Brazil Richarlison ya ci kwallon da aka zaba a matsayin kwallo mafi kyau a gasar cin kofin duniya ta 2022 da aka kammala a Qatar.

 

Richarlison dai shi ne yaci kwallo ta biyu a wasan da Brazil ta do ke Serbia a wasan rukuni na G da suka kece raini da juna.

 

Kuma Kwallon wadda Richarlison ya ci ya samu taimakon Dan wasa Vinicius Jr, wanda hakan ya sanya Kwallon ta zama mafi Kyau da kayatarwa da aka zaba.

 

Kwamitin kasa da kasa na gudanarwa a Hukumar kwallon kafa na duniya (FIFA) ne dai ya zabi kwallon.

 

Kwallon da Richarlison ya zura ta do ke wadda Yan wasa irinsu Kylian Mbappe, Neymar, Cody Gakpo, Vincent Aboubakar suka zura.

 

Haka zalika kwallon ta doke wadda Luis Chavez, Enzo Fernandez, Paik Seung-ho, da Salem Al-dawsari duka suka zura a gasar.

 

Kuma a jumlace dan Richarlison ya zura kwallo uku a wasa hudu da ya fafata a kofin duniya a Qatar 2022.

Latest stories

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...