Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniKasar Portugal na shirin nada Mourinho sabon mai horar da tawagar

Kasar Portugal na shirin nada Mourinho sabon mai horar da tawagar

Date:

Hukumar kwallon kafa ta kasar Portugal PFF na duba yiwar nada Jose Mourinho sabon mai horar da tawagar.

 

Jose Mourinho dai yanzu haka shi ne ke horar da kungiyar kwallon kafa ta AS Roma da ke kasar Italiya.

 

Kuma matakin na zuwa ne bayan da hukumar PFF ta ce zata maye gurbin Fernando Santos da Mourinho, bayan da ya jagoranci kasar a kofin duniya A Qatar, da Portugal ta fice a matakin dab da kusa da karshe.

 

Jose Mourinho nada ragowar kwantargi da Roma har zuwa shekarar 2024, sai dai lokaci ne kadai zai rabe yadda wannan lamarin ka iya gudana.

 

Jaridar Sky Sport da ke Italiya ce ta rawaito cewa, hukumar PFF na ci gaba da matsa lamba ga Mourinho domin ya amshi aikin horar da tawagar.

 

A baya dai a watan Yuli Mourinho ya taba jagorantar tawagar matasa ta kasar Yan kasa da shekara 21 amma na rikon kwarya.

 

Jose Mourinho wanda ya koma Roma a shekarar 2021, ya jagoranci kungiyar lashe UEFA Conference League a karon farko, tin bayan shekaru da dama kungiyar bata lashe wata gasa a nahiyar ba.

 

Kuma a baya Jose Mourinho ya jagoranci kungiyoyi irinsu Chelsea da Real Madrid da Inter Milan da Tottenham Hotspur da FC Porto da kuma Manchetser United.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...