Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniMorocco Za ta karbi bakuncin gasar FIFA Club World Cup ta 2023

Morocco Za ta karbi bakuncin gasar FIFA Club World Cup ta 2023

Date:

Shugaban hukumar kwallon kafa na duniya duniya Giano Infantino ya ce Morocco ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kungiyoyin duniya wato Club World Cup.

 

Infantino ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da yayi a birnin Doha na kasar Qatar a ranar Juma’a.

 

Infantino ya kuma ce gasar za ta fara gudana daga ranar 1 ga Fabrairu zuwa 11 ga watan na shekarar badi.

 

Gasar wadda ta kasance karo na 24 akalla kungiyoyin duniya ne takwas ne zasu kece raini da juna.

 

Har ma Infantino ke bayyana nan da gasar shekarar 2025 ana duba yiwuwar mayar da gasar zuwa kungiyoyin duniya 32.

 

“Matuka muna saran gasar shekarar 2025 za ta kasance kungiyoyin duniya 32 ne zasu halarta, hakan da ke nuni cewa za ta zama gasar kofin duniya wato World Cup.” a cewar Infantino.

 

Morocco dai ta karbi bakuncin gasar Club World Cup a shekarar 2013 da 2014.

 

Amma gasar da ta gudana a baya an fafata hadaddiyar daular larabawa a watan Fabrairu wadda Chelsea ta lashe.

 

Real Madrid, itace wadda ta lashe gasar a shekarar 2014 a kasar Morocco, kuma yanzu haka tana cikin kungiyoyin da zasu fafata a gasar bayan lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a kakar da ta gabata.

 

Ana saran Flamengo daga Brazil, Al Hilal daga Saudi Arabia, Wydad Casablanca daga Morocco, Seattle Sounders daga United States da New Zealand’s Auckland City sune dai zasu kece raini da junansu a gasar ta Club World Cup.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories