Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniAbin da ya kamata ku sani a wasan Faransa da Argentina

Abin da ya kamata ku sani a wasan Faransa da Argentina

Date:

Wannan Lahadin 18 ga Disambar da muke ciki ta tabbata ranar karshe ta rufe gasar cin kofin duniya ta 2022 da ke gudana a Qatar.

 

Wato Faransa da Argentina, zasu buga wasan karshe na gasar, Messi da Mbaffe zasu kara da juna a filin wasa na Lusail da ke Qatar karkashin jagorancin Symon alkalin wasa dan kasar Poland.

 

Wato bari mu kalli wasu abubuwa mahimmai tsakanin kasashen biyu, Argentina zata buga wasan karshe na kofin duniya sau 6 a tarihi, da kasar Jamus ce tafi yawan buga wasan na karshe da jumulla 8.

 

Cikin wasa 6 na karshe da Argentina ta kai ta lashe biyu a shekarun 1978 da 1986, wanda take fatan lashe gasar a karo na uku a tarihi.

 

Amma fa idan tayi rashin nasara to zata bi samun Jamus wadda tafi rashin nasara a wasan karshe a gasar da jumulla 4.

 

Mu kalli Faransa kuwa ta kai wasan karshe a gasar har sau hudu, da (1998, 2006, 2018, da kuma shekarar da muke ciki ta 2022).

 

Amma Faransa na shirin kafa tarihin zama kasa ta uku da zata zo da kofin kuma ta koma da shi, wato a turance back-to-back World Cups wining, bayan Italiya wadda tayi a shekarun (1934 da 1938) sai kuma Brazil (1958 da 1962).

 

Sai dai fa wannan wasan karshen tsakanin Faransa da Argentina shi ne zai zama hadu ta hudu da kasashen sukayi da junansu a wannan gasa ta kofin duniya.

 

Kuma Argentina ta lashe wasa biyu cikin ukun da suka buga a baya, amma Faransa lashe wasa daya kawai tayi a 2018 a zagayen kwaf daya wato round of 16.

 

To sai dai sun hadu sau 13 a duka haduwa da sukayi a wasa daban-daban, da Faransa ta lashe wasa uku ciki kawai, Argentina ta lashe 6 akayi canjaras guda 3.

 

Amma Faransa cikin wasa 10 baya a wasa da kasashen kudancin Amurka ba tayi rashin nasara ba, domin kuwa ta samu nasara sau 6 kunnan doki 4.

 

Inda wannan karawar itace wasan karshe na 11 a kofin duniya da kasashe na yankin Kudancin Amurka da na yankin nahiyar turai za su fafata da juna, amma kasashen yankin kudancin amurca cikin 10 sun lashe 7 daga ciki.

 

Mu kalli dan wasan Argentina Lionel Messi, zai zama na farko da ya fi kowa buga gasar cin kofin duniya da jumulla 26 idan har ya buga wasan karshen na bana.

 

Sannan ya zama dan wasa na farko a gasa daya da ya zura kwallo a matakin rukuni, da matakin kwaf daya wato round of 16, da matakin dab dana kusa da karshe, da matakin kusa da karshe.

 

Wai… Messi kenan, idan ya zura kwallo a wasan karshe fa, babu wani dan wasan a duniya da ya yi wannan bajintar sai shi…

 

Messi kawo yanzu ya zura kwallo 11 da taimakawa aka zura kwallo 8 a wasan kofin duniya 25 da ya buga, idan ya ci kwallo daya zai zama na farko shi kadai da ya ci kuma ya taimaka aka sanya kwallo 20 a raga, kenan ya kamo tarihin da akayi a shekarar 1966.

 

Kuma Antoine Griezmann da Kylian Mbappé a baya a gasar 2018 a Rasha kowa cikinsu ya ci kwallo a wasan karshe da Faransa ta doke Crotia da ci 4-2, kenan idan kowa a cikinsu ya zura kwallo zasu kamo tarihin da …..

 

‘Yan wasa 4 ne kawai sukai Wannan bajintar zura kwallo sau biyu a wasan karshe na kofin duniya biyu daban-daban.

 

Wadannan yan wasan kuwa su ne Vavá (1958, 1962), Pelé (1958, 1970), Paul Breitner (1974, 1982), da Zinedine Zidane (1998, 2006).

 

Kylian Mbappé zai zama dan wasa mai shekara 23 da kwanaki 363 da zai lashe kofin duniya biyu daban-daban, amma idan har Faransa ta lashe gasar.

 

Kuma a shekarunsa 44 a duniya mai horar da kasar Argentina Lionel Scaloni zai zama matashin mai horarwa na farko da ya jagoranci kasa zuwa wasan karshe a kofin duniya.

 

Bayan da Rudi Voller a shekarar 2002 a lokacin yana da shekara 42, da kuma Cesar Luis Menotti da shi kuma yana shekara 39 a gasar da akayai a shekarar 1978 ya jagoranci kasa zuwa wasan karshe.

 

Daga bangaren mai horara da Faransa Didier Deschamps zai zama na biyu cikin jerin masu horarwa da suka jagoranci kasa zuwa wasan karshe bayan Vittorio Pozzo da ya jagoranci Italiya zuwa wasan karshe biyu a shekarun 1934 da 1938.

 

Hugo Lloris mai tsaran raga na Faransa zai zama na hudu kyaftin da ya jagoranci wata kasa zuwa wasan karshe biyu daban-daban, bayan Karl-Heinz Rummenigge (1982 da 1986), sai Diego Maradona (1986 da 1990) da kuma Dunga (1994 and 1998).

 

Yanzu tsakanin Kylian Mbappé matashin dan wasa kuma mai jini a jika, da kuma Lionel Messi jagoran masu sanya gajeran wando a fagen kwallon kafa kuma tsoho mai ran karfe waye kuke gani zai lashe kofin duniya.

 

Gasar ta shekarar 2022 da Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino ya ce Ba a taba gasar kofin duniya da ta kayatar ba kamar wadda ake a Qatar.

 

Infantino da ya ce duka kasashen da suka samu halartar gasar su 32 sun bar Qatar da ke Gabas ta Tsakiya da wani abun alkhairi da ba zasu taba mantawa ba.

 

To amma daga gasar 2026 ana shirin sauya gasar zuwa kasashe 48 daga 32 da akai a Qatar din.

 

An dai sauya fasalin kara gasar tin a shekarar 1998 wanda daga nan ne FIFA ta fadada gasar kofin duniya zuwa kasashe 32.

Latest stories

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...