Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniWorld Cup: Buhari ya taya Morocco murnar kafa sabon tarihi ga Nahiyar...

World Cup: Buhari ya taya Morocco murnar kafa sabon tarihi ga Nahiyar Afrika

Date:

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga tawagar kasar Morocoo, na kafa sabon tarihi ga nahiyar Afrika a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.

 

Shugaban ya mika sakon ne ga al’ummar kasar Morocco, da kuma Sarkin kasar Muhammad bisa wannan nasarar da tawagar ta samu.

 

A wata sanarwa da hadimin shugaban ya fitar Garba Shehu a wannan rana ta Litinin a birnin tarayya Abuja, ya ce Buhari ya mika sakon jinjina ga tawagar ta Atlas Lions bisa bajintar da su kayi.

 

Kasar Morocoo dai kawo yanzu ta zama kasa ta farko daga Nahiyar Afrika da ta kai zagayen kusa da karshe a gasar cin kofin duniya a tarihi.

 

‘Matuka abin da Morocco tayi abin aya ba ne, kuma ta zama abin alfahari ga duka kasashen nahiyar Afrika, du ba da cewa tayi abin da babu wata kasa da ta yi irin hakan,’ a cewar Sanarwar da Garba Shehu ya fitar.

 

Kawo yanzu dai tawagar ta Atlas Lions a gasar da ke gudana a yanzu haka a Qatar, Morocoo za ta fafata da kasar Faransa a matakin kusa da karshe a gasar ta kofin duniya ta shekarar 2022.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories