Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanni1 Year Anniversary: Premier Radio ta doke Aminchi Radio a wasan karshe

1 Year Anniversary: Premier Radio ta doke Aminchi Radio a wasan karshe

Date:

Yan wasan kungiyar kwallon kafa na Premier Radio 102.7 sun lashe gasar da aka sanya domin taya tashar murnar cika shekara da kafuwa.

 

Wasan ya gudana a ranar Lahadi, tsakanin kungiyoyin kafafen yada labarai uku da suke jihar Kano, wanda a karshe Premier Radio ta lashe gasar bayan doke Aminci da ci 2-1.

 

Akalla dai kungiyoyi hudu aka tsara zasu fafata a gasar, sai dai uku ne suka halarci gasar da suka hada Aminci Radio da Express da kuma Premier Radio.

 

Wasan dai kowacce kungiya ta buga wasa biyu, inda a karshe Premier Radio tayi nasarar lashe gasar bayan samun maki hudu a duka wasanni biyun.

 

Tashar Premier Radio 102.7 a wannan rana ta Lahadi 11 ga Dismabar 2022, take bikin cika shekara 1 da fara gabatar da shirye-shirye a jihar Kano.

Latest stories

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...