Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSha'aban Sharada ya kaddamar da takarar neman gwamnan Kano

Sha’aban Sharada ya kaddamar da takarar neman gwamnan Kano

Date:

“Abdullahi Abbas da gwmanan Kano Ganduje sunce naci taliyar karshe kuma ni nasan Allah ne keyin komai.

“Abin takaici ace tunda aka fara mulki amma har yanzu akwai yankunan da suke fama da matsalar ruwan sha wanda matsala ce da ya kamata ace tuni an magance ta.

Ya kuma ce ba sai wani ya tsaya masa ba zayyi takarar gwamna a jihar Kano a don haka ya bukaci alummar jihar Kano da su goya masa baya don ceto su daga halin da suka tsinci kansu a sanadiyar masu mulkin kama karya.

Kotu a Kano ta sassauta sharudan belin Dan Bilki Kwamanda
Kan batun rabon kayan tallafin Ya ce kayayyakin da suka rabawa matasan zasuyi amfani dasu ne wajen gudanar da sana’o’in dogaro dakai.

Ya kuma ce sun biyawa direbobin adaidaita sahu naira dubu biyar biyar na tarar da gwamnatin jihar Kano taci su ba bisa ka’ida.

Shima da ya kasance a gurin taron sanatan Kano ta Tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya bukaci wadanda suka amfana da tallafin da suyi amfani dashi ta hanyar da ta dace domin dogaro da kansu.

Malam Ibrahim shekarau ya kara da cewa babu wani dan majalissar wakilai ta tarayya da ya taba rabon kayan tallafi makamancin na Sha’aban Ibrahim Sharada.

Malam Ibrahim Shekarau ya kuma bukaci ‘yan siyasa da suyi koyi da irin aikace aikacen sa domin ciyar da matasa gaba a jihar nan da kasa baki daya.

Cikin wadanda suka samu halartar taron dai akwai Abdulmajid Danbilki Kwamanda da Shehu Usman Dalhatu da Ahmadu Haruna Zago da kuma wakilin injiniya Rabi’u Musa Kwankwanso Alhaji Danyaro Yakasai da sauran manyan baki.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...