Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu a Kano ta sassauta sharudan belin Dan Bilki Kwamanda

Kotu a Kano ta sassauta sharudan belin Dan Bilki Kwamanda

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Kotun Majistare a Kano ta sassauta sharudan belin da ta sanyawa Abdulmajin Dan Bilki Kwamanda.

Kotun karkashin mai Shari’a Aminu Gabari ta sassauta sharudan ne ranar Alhamis bisa rokon da lauyan Dan Bilki ya yayiwa Kotun.

Idan za a iya tunawa dai gwamnatin Kano ce ta gurfanar da dan Bilki kwamanda bisa zargin Bata mata suna.

a zaman kotun na bayan kotun ta nemi Dan Bilki ya gabatar d wadanda za su tsaya masa da suka hadar da wakilin Gabas da kuma limamin Masallacin hajiya Mariya da ke Koki.

Sai dai a zaman kotun na yau Lauyansa Barr. Funsho ya bukaci kotun da ta sake duba sharuddan da ta gindaya a baya.

Ya ce wanda ake kara zai ci gaba da zuwa kotu domin sauraren laifukan da ake kararsa akai.

Da yake martani kan batun Lauyan gwamnati Barr. Wada Ahmad Wada, ya ce batun sake duba belin na hannun kotu.

Sai dai ya yi fatan za a bi ka’idojin shari’a da adalci wajen sake nazarin.

A hukuncin da ya yanke, Alkalin kotun ya umurci Danbilki da ya gabatar da mutane 2 wadanda suka hada da: mahaifinsa ko wakilinsa, maimakon Wakilin Gabas na masarautar Kano da aka bukata tun da fari

Hakazalika, kotun ta umurci wanda ake kara da ya gabatar da limamin duk wani masallaci da ke unguwar Koki, ko kuma limamin kowane masallacin da ya ke gudanar da sallarsa a wajen.

Mai Shari’a Gabari ya kuma ba da umarnin cewa, haka nan wanda ake tuhuma zai iya kiran duk wani shugaban addini a cikin al’umma, idan har bai samu wani Imami da zai tsaya masa ba.

Wannan ya maye gurbin Babban Limamin Masallacin hajiya Mariya Sanusi Dantata da ke unguwar koki da kotun ta ambata a baya.

Sannan kotun ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga Afrilu, 2023 don ci gaba da ambato.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...