Saurari premier Radio
24.2 C
Kano
Monday, September 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWani soja ya hallaka fararen hula 3 da jikkata 13 a Borno

Wani soja ya hallaka fararen hula 3 da jikkata 13 a Borno

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wani sojan kasar nan da ake zargin yana tu’ammali da miyagun kwoyoyi ya harbe akalla fararen hula uku har lahira kuma ya raunata wasu mutum 13 yayin wani harbin mai-uwa-da-wabi da ya yi.

Wannan al’amarin ya auku ne a tsakiyar garin Mafa da ke jihar Borno.

Ganau sun ce cikin wadanda sojan ya halaka, akwai wata yarinya ‘yar shekara uku, sannan sauran mutum 13 na asibiti inda ake kula da su saboda raunukan da suka samu daga harbin da ya yi musu.

Wani rahoto ya ce sojan na cikin sojojin Najeriya da aka tura yankin domin yakar ‘yan kungiyar Boko Haram da na ISWAP.

Shaidu sun kuma ce an yi nasarar kwace bindigar daga hannun sojan kuma a halin yanzu yana hannun hukumomin soji.

Sai dai rundunar sojojin kasar nan ba ta ce uffan ba dangane da al’amarin.

Latest stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...