24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiSha'aban Sharada ya kaddamar da takarar neman gwamnan Kano

Sha’aban Sharada ya kaddamar da takarar neman gwamnan Kano

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Dan majalissar wakilai ta tarayya mai wakiltar karamar hukumar birnin Kano Sha’aban Ibrahim Sharada ya kaddamar da takarar sa ta neman zama gwamnan jihar Kano a zaben badi a jam’iyar APC.

Sha’aban Sharada ya kaddamar ta takarar tasa yayin rabon tallafin kayan sana’a da motoci da kudi da kuma takardun daukar aiki wanda mutane fiye da dubu ashirin suka amfana.

Yayin taron da akayi a Alhamis din nan a filin wasa na Polo Sha’aban Sharada ya ce matukar ya zama gwamnan jihar Kano zai samar da birane makamantan Kano guda shida tare da aiwatar da aikace aikace da za’ayi alfahari dasu fiye da shekaru dari masu zuwa.

Yan Kwankwasiyya sun mamaye babban zaben NNPP a Kano
Ya ce ya fito takara ne duba da abubuwan da akeyi ba daidai ba a mulkin jihar Kano. Ya kara da cewa matukar yaci zabe zai gina sabbin kasuwanni tare da inganta fannin noma da ilimi da kuma lafiya.

Latest stories