Mukhtar Yahya Usman
Dubban yan Kwankwasiyya ne suka mamaye harabar wurin da Jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari za ta gudanar da baban zabenta.
An dai tsara gudanar da zaben ne a cibiyar koyar da Sana’o’i ta sani Abacha wato Abacha Youth Center da ke kan hayar Madobi.
Ana sa ran Jam’iyyar za ta zabi shugabaninta a mataki daban daban ayau Litinin.
Sai dai abinda ke jan hankali a wurin taron shi ne yadda magoya bayan Kwankwasiyya suka mamaye wurin.
Wannan dai baya rasa nasaba da yadda ake ta rade-radin jagoran Kwnkwasiyyar Rabiu Musa zai koma cikin Jam’iyyar.
Idan za a iya tunawa dai tun a watan da ya gabata ne Jam’iyyar ta rushe shugabancinta, tare da kafa kwamitin riko.
A yau Litinin ne dai aka tsara gudanar da zaben shugabannin Jam’iyyar da kuma ake ganin yan Kwnkwasiyya ne suka mamaye dukkanin mukaman da za zaba.