Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSalihu Tanko Yakasai ya fice daga APC

Salihu Tanko Yakasai ya fice daga APC

Date:

Tsohon mashawarcin gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya fice daga jam’iyyar APC Saboda Rashin sauke alkawuran da ta yiwa al’ummar Kasar nan.

Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne yayin taron Manema labarai a nan kano.

Yakasai wanda ake yiwa lakabi da Dawisu yace Jam’iyyar APC ta gaza sauke mafi yawa daga cikin nauye-nauyen data daukarwa yan Nigeria.

“Da ni aka yi tallan jam’iyyar APC a dukkanin mafi yawa daga cikin jihohin Nigeria , Kuma mun yiwa al’ummar kasar nan alkawura Amma ni da kaina na gamsu da cewa jam’iyyar ta gaza dauke alkawuran data yiwa yan kasa”. Inji Salihu Tanko Yakasai

Salihu Yakasai Wanda Gwamnatin kano ta sauke daga mukaminsa Saboda irin kalaman da yake yiwa gwamnatin tarayya ya ce ya dade yana fadawa gwamnatoci gaskiya tun lokaci da PDP ta ke Kan mulki.

“Saboda irin Matsalolin da yan Ƙasar nan suke ciki na rashin tsaro, rashin baiwa yan kasa kyakykyawar rayuwa ,sanya yan kasa cikin Mawuyacin halin dama wasu matsalolin, hakan tasa na fice daga jam’iyyar APC a wannan rana”.inji Salihu Yakasai

Salihu Tanko Yakasai yace nan gaba kadan zai bayyana inda zai koma domin cigaba da gwagwarmayar siyasa.

Latest stories

Related stories