Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoYanzu-Yanzu:Kwamishin Ganduje yayi murabus

Yanzu-Yanzu:Kwamishin Ganduje yayi murabus

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Kwamishinan al’amuran ruwa na jihar Kano Sadiq Wali yayi ritaya daga mukaminsa na Kwamishinan.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan ya fitar ranar Alhamis.

Kwamishinan ya ce ya ajiye mukamin nasane sakamakon takarar siyasa da zai tsaya.

Ya kuma godewa gwamna Ganduje bisa damar da ya bashi na zama Kwamishinan har tsahon Shekaru biyu.

Ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da baiwa gwamna Ganduje hadin Kai wajen gudanar da al’amura gwamnati da zarar an bukaci hakan.

Da yake karbar takardar ritayar tasa mukaddashin gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya ce gwamnati ta gode da aikin Kwamishinan.

Ya ce a tsahon shekaru biyu da kwamishinan ya dauka yana aiki ya bunkasa bangaren ruwa sosai da sosai.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...