Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaSama da mutane dubu 23 ne suka kamu da cutar kwalara a...

Sama da mutane dubu 23 ne suka kamu da cutar kwalara a kasar nan

Date:

Kimanin mutane dubu ashirin da uku da dari biyar da hamsin (23,550) ne ake zargin sun kamu da cutar kwalara, yayin da mutum dari biyar da tamanin da uku (583) suka rasa rayukansu sakamakon cutar.

 

Hakan na kunshe ta cikin rahoton da hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta fitar.

 

Rahoton ya bayyana cewa an samu mutuwar mutanen 583 ne a kananan hukumomi 270 na jihohi 32 a fadin kasar, ciki har da Abuja.

 

Dr. Abdullahi Bulama, daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar lafiya matakin farko na kasa. Yace hukumar na aiki tukuru domin shawo kan wannan al’amari.

 

Dr. Bulama ya bada shawarar dawo da ‘yan duba gari domin tabbatar da tsafta, wanda hakan zai iya rage yaduwar cututtuka tsakanin jama’a.

 

Gurbacewar muhallin da aka samu sanadiyar ambaliyar ruwa a damunar bana na daga cikin abubuwan da suka  haddasa barkewar cutar ta kwalera.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...