Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn yi sulhu da direbobin tankar da suka rufe hanyar Kano zuwa...

An yi sulhu da direbobin tankar da suka rufe hanyar Kano zuwa Zaria

Date:

Hafsat Nasir Umar

 

Direbobin tankar da suka tare hanyar Zariya zuwa Kano bayan wani soja ya halaka guda daga cikin direbobin sun saki hanya.

 

A Asabar din nan, direbobin suka amince su janye motocin nasu da suka tare hanyar bayan tattaunawa da jami’an tsaro da kuma jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC).

 

Lamarin dai ya haifar da cunkoson ababen hawa tsawon kwanaki, inda mutane suka koma amfani da wasu hanyoyin, wasu kuma da dama suka yi curko-curko.

 

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai rikon mukamin Kwamandan FRSC na Jihar Kaduna, Lawal Garba, ya ce yanzu lamura sun daidaita a hanyar.

 

Tuni Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da kaddamar da cikakken bincike kan kisan da sojan yayiwa direban, wanda shi ne ya haddasa rufe hanyar tun da farko.

Latest stories

Related stories