
Ishaq Sani Dambazau
Wata mummunan gobara da ta tashi bayan tankar dakon man fetur ta yi haɗari a Jihar Cross River ta yi sanadin mutuwar mutum ɗaya, yayin da wani mutum ya samu munanan raunuka, tare da ƙone shaguna, gidaje da motoci da dama.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026, a kan babbar hanyar Calabar zuwa Odukpani, kusa da hedikwatar ƙaramar hukumar Odukpani.
Jaridar punch ta rawaito cewa tankar, wadda ke ɗauke da fiye da lita 45,000 na man fetur, ta yi fama da matsalar birki a kusa da wani shingen rage gudu, lamarin da ya sa ta kife tare da zubar da man da take ɗauke da shi, wanda daga bisani ya kama da wuta.
Wutar ta bazu zuwa shaguna da gine-ginen da ke kusa, tare da lalata motoci da dama. Rahotanni sun kuma nuna cewa wutar ta ƙara ƙamari bayan man da ya zuba ya isa wani tiransfoma na wutar lantarki da kuma wata babbar mota da aka ajiye a yankin.
Rundunar ’yan sandan Jihar Cross River ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakinta, Sunday Eitokpah, ya ce an ceto direban tankar daga cikin wutar tare da garzayawa da shi asibiti domin kula da lafiyarsa, sai dai daga baya rundunar ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya da kuma jikkatar wani mutum.
Jami’an ’yan sanda da na kashe gobara sun isa wurin domin shawo kan lamarin da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Rundunar ta kuma buƙaci mazauna yankin da masu ababen hawa da su nisanci wurin domin bai wa jami’an agajin gaggawa damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
