Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, da amfani da rasuwar mahaifiyarsa wajen neman tausayi a siyasa, yana mai cewa bai kamata ya shigar da marigayiyar cikin muhawarar siyasa ba.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Asabar, yayin da yake jawabi ga mambobin Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta Uzugbani Ekpeye, a Ahoada ta Gabas, Jihar Rivers.
Martanin nasa na zuwa ne bayan Amaechi, wanda ke takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Channels cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun taimaka wajen mutuwar mahaifiyarsa, saboda tsadar magunguna ta sa ya kasa sayen waɗanda take buƙata.
Wike ya soki wannan furuci, yana mai tambayar yadda Amaechi, wanda ya taɓa zama kakakin Majalisar Dokokin Jihar Rivers, gwamnan jihar da kuma ministan sufuri, zai ce ya kasa biyan kuɗin magungunan mahaifiyarsa.
Ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa tsohon gwamnan bai nemi taimakon abokansa da sauran makusantansa ba, idan har ya fuskanci matsalar kuɗi wajen kula da mahaifiyarsa.
Ministan ya kuma soki yadda Amaechi ya danganta farin cikin mahaifiyarsa da nasarar ADC a zaɓen 2027, yana mai cewa bai dace a yi amfani da ƙaunataccen da ya rasu wajen jawo hankalin masu zaɓe ba.
Sai dai waɗannan kalamai na Wike sun ƙara rura wutar takun saƙa da ke tsakanin manyan ’yan siyasar biyu, waɗanda suka daɗe suna hamayya tun lokacin da suke gudanar da harkokin siyasa a Jihar Rivers.
