Ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara ta fara gudanar da wani shirin kai agajin gaggawa daga gida zuwa gida domin yaƙi da barkewar cutar Diphtheria a ƙaramar hukumar Gusau.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar, Suleiman Isah, ya fitar, inda ya ce shirin na gudana ne tare da tallafin ƙungiyar agaji ta likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF).
Sanarwar ta bayyana cewa manufar shirin ita ce ƙarfafa ƙoƙarin gano waɗanda ake zargin sun kamu da cutar tun da wuri, da ɗaukar matakan dakile yaɗuwarta, tare da tabbatar da cewa an gaggauta kai waɗanda ake zargi da kamuwa da ita zuwa cibiyoyin lafiya domin samun kulawar da ta dace.
Ma’aikatar ta ce kai ziyara gidaje zai taimaka wajen wayar da kan al’umma game da alamomin cutar da kuma muhimmancin neman agajin likita da zarar an ga alamun kamuwa da ita, maimakon jira har sai yanayin mara lafiya ya tsananta.
Cutar Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ƙwayoyin cutar ke haddasawa, kuma tana iya shafar maƙogwaro da hanyoyin numfashi, idan ba ayi gaggawar magance ta ba, tana iya haifar da matsaloli masu tsanani ga lafiyar wanda ya kamu da ita.
Jihar Zamfara ta ce za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki domin kare al’umma daga cutar, tare da ƙarfafa matakan gano waɗanda suka kamu da ita da kuma hana ci gaba da yaɗuwarta.
