Saurari premier Radio
24.7 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMutane biyu 'yan bindiga suka sace mana ba 14 ba cewar mutanen...

Mutane biyu ‘yan bindiga suka sace mana ba 14 ba cewar mutanen kauyen Yola dake Karaye a nan Kano

Date:

Al’ummar kauyen Yola dake karamar hukumar Karaye sun ce mutane biyu aka sace a kauyen ba goma sha daya ba kamar yadda ake fada.

A ziyarar gani da ido da Premier Radio ta kai kauyen na Yola a ranar Talata al’ummar garin sun tabbatar da faruwar lamarin saidai sunce sau daya ‘yan bindigar suka shiga kauyen na Yola.

Sun bayyana mana cewa tunda fari dai ranar Alhamis wasu mutane sunje wani gida a kauyen, a zuwan su na farko dai sunje ne da nufin su tafi da mai gidan saidai basu same shi ba sai suka tafi da daya daga cikin yayan gidan da matar mai gidan bayan sunyi harbe-harbe.

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane da dama tare da kashe wasu a garin Yola dake karamar hukumar Karaye dake nan jihar Kano.

Wadanda muka tattauna dasu sunce yan bindigar sun so suyi garkuwa da mai gidanne amma basu yi nasara ba.
Sai dai bayanai daga gurin mutanen garin da iyalan mutumin sunce yan bindigar sun kirasu a waya suna neman su basu naira miliyan goma domin su saki wadanda sukayi garkuwa dasu.

Zuwa yanzu dai daya daga cikin wadanda sukayi garkuwa dasu ya kubuto inda suka harbe shi har sau biyu.

Yayin da kuma suka rike mutane biyu da suka kai musu kudin fansa naira miliyan biyu saidai daga bisani sun sako mutum daya inda yanzu haka mutane biyu ke cigaba da kasancewa a hannun su wato matar mutumin da kuma daya daga cikin wadanda suka kai kudin fansar tunda fari.

Kuma wadanda muka zanta dasu sunce masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa naira miliyan hamsin domin sakin mutane biyun dake hannun su.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...