Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCibiyar rahoton bincike ICIR ta gudanar da horon karfafa alakar Yan jarida...

Cibiyar rahoton bincike ICIR ta gudanar da horon karfafa alakar Yan jarida da Yan kungiyar fararen hula

Date:

Cibiyar rahoton bincike ta kasa da kasa ICIR ta horar da Yan jarida da Yan kungiyar fararen hula game da yanda zasuyi aiki hannu da hannu wajen tabbatar da an gudanar da gwamnati bisa tsarin daya dace.

Akalla Yan jarida 20 da Yan kungiyar fararen hula 20 ne suka halarci horon daga jihohin Arewa daban-daban da aka gudanar a nan Kano

Mahalarta taron tun tattauna game da matsalolin dake kawo tasgaro wajen haddin gwiwwar bangarorin biyu yayin gudanar da ayyukansu dake da alaka da juna.

Shugaban cibiyar Dayo Aiyeten ya gabatar da mukala game da muhimmancin hadin gwiwwar bangarorin biyu wajen yakar cin hanci da rashawa da rashin adalci a bangaren gwamnati.

Dayo ya kara da cewa Yan jarida suna da matukar muhimmancin wajen tabbatar da dorewar dimokradiyyar Najeriya.

An horar da mahalarta game da yanda zasuyi amfani da kafafen sada zumunta wajen wayar da kan alumma da kusoshin gwamnati game da matsalolin da suka addabi alumma.

Mahalartan sun sha alwashin yin amfani da abunda suka koya wajen inganta ayyukansu a nan gaba.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...