Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Kano za ta koyawa tubabbun Yan Daba 222 sana'o'in dogaro da...

Gwamnatin Kano za ta koyawa tubabbun Yan Daba 222 sana’o’in dogaro da kai

Date:

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana gwamnatinsa Za ta koyawa tubabbun Yan Daba 222 kananan sana’oin dogaro da kai.

Abba Kabiru Yusuf ya bayyana hakan a taron yaye tubabbun ‘yan daba 50 wadanda suka samu mukamin kwansitabul na ‘yan sanda.

Yusuf ya ce tuni gwamnatinsa tayi shirin sake koya musu kananan sana’oin dogaro da kai musamman yadda suke kokarin kawo jihar zaman lafiya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda reshen Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar rana

A ranar Litinin ne dai rundun yan sandan Kano ta ce tubabbun Yan Daban na cikin ‘yan daba 222 da suka yi saranda ga ‘yan sanda tare da daukar alkawarin ba za su sake aikata laifi ba.

Jumullar mutum 50 din da aka dauka aikin dai sun fito ne daga kananan hukumomin Dala da Fagge da Ungogo da Municipal da kuma Gwale da suka zama.

Rundun yan sandan ta ce sabbin ma’aikatan sun samu horo na watanni biyu kafin suka samun mukamin kwansitabul din.

Cikin wadanda suka halarci wannan taron sun hadar da kwamishinin Yan Sanda Kano CP Muhammad Usaini Gumel da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Da ma shugaban gidauniyar AMG Dr Aminu Garba Magashi.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...