Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar Dokokin Kano, Ta Gudanar Da Taron Jin Ra’ayoyin Al’umma Kan Kasafin...

Majalisar Dokokin Kano, Ta Gudanar Da Taron Jin Ra’ayoyin Al’umma Kan Kasafin Kudin 2024

Date:

Kungiyoyi masu zaman kansu da na cigaban al’umma sun bukaci gwamnati da majalisar dokokin jihar Kano su tabbata an aiwatar da muhimman ayyukan da aka tsara a fannin ilimi da lafiya da noma da samar da ruwan sha da hanyoyi da kuma samar da cibiyoyin bai wa mata da matasa horon sana’o’in dogaro da kai.

Sun bayyana bukatar ne yayin taron jin ra’ayoyin al’umma da majalisar dokokin Kano ta gudanar kan kasafin kudin jihar Kano na shekarar 2024.

Dr. Kabir Hamisu Kura na kungiyar tabbatar da adalci a bangaren ilimi, ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara adadin kudin gudanar da bibiyar ayyukan makarantu da bai wa malamai horo da samar musu da ababan hawa da muhalli da kayan aiki da kuma kulawa da walwalarsu da ta masu bibiyar aikinsu.

Ita kuwa Dr. Maryam Garba Umar, ta cibiyar kare hakkin dan Adam da harkokin ilimi, ta bukaci gwamnati ta kara kulawa da gidan yara na Nassarawa da na gajiyayyu da na masu tabin hankali da na gyaran tarbiyya da cibiyar kula da masu yoyon fitsari musamman kula da lafiyarsu da ilimi da kuma ba su horo akan sana’o’in dogaro da kai.

Shugaban masu rinjaye na majalisar kuma shugaban taron, Lawan Hussaini Cediyar Yan Gurasa wanda ya ya bayar da gudummawar da mahalarta taron suka bayar, ya ce a shekarar da ta gabata majalisar da kara fiye da Naira miliyan dubu daya a kan kasafin kudi a sakamakon bukatun al’umma a irin wannan taro inda ya ba da tabbacin kamanta irin haka idan bukatar hakan ta taso.

Wakilinmu, Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa da yake jawabi bayan sauraron ra’ayoyin kungiyoyi 35, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kasafi kuma wakilin karamar hukumar Minjibir, Abdul Abdulhamid, ya ce za su tace bukatunsu tare da yin amfani da wadanda suka dace.

Latest stories

Related stories