Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKotun Koli Ta Umarci A Ci gaba Da Tsare Jagoran Kafa Kasar...

Kotun Koli Ta Umarci A Ci gaba Da Tsare Jagoran Kafa Kasar Biafra, Bayan Ta Tabbatar Da Tuhumar Cin Amanar Kasa Da Ake Masa.

Date:

Kotun koli ta tabbatar da tuhumar cin amanar kasa da ake yi wa Shugaban Kungiyar masu fafutukar kasar Biafra, da ke neman ballewa da Najeriya, Nnamdi Kanu.

A shekarar 2015 ne aka fara tsare Nnamdi Kanu, sai dai bayan kotu ta bayar da belinsa ya tsere daga Najeriya zuwa kasar Birtaniya bayan wani hari da sojoji suka kai gidansa.

Bisa kamo shi ba busa ka’ida ba ne ta sa kotun daukaka karar ta umarci gwamnati ta sake shi, hukuncin da gwamnatin ta daukaka kara a kai.

Sai dai kotun kolin ta ce duk da cewa an dawo Nnamdi Kanu Najeriya ba bisa ka’ida ba daga kasar Kenya, a lokacin da ya gudu daga beli, amma hakan ba zai iya hana kotun shari’ar ta ci gaba da shari’a ba.

Saboda haka kotun kolin ta soke hukuncin kotun daukaka kara da ta bayar da umarnin sakin sa a baya.

A hukuncin kotun na Juma’ar nan, alkalanta biyar sun ce kotun daukaka kara tana da hurumin gurfanar da shi.

Ta bayyana cewa saba ka’ida wajen dawo da shi Najeriya daga kasar wajen ba zai soke tuhumar da ake masa ba.

A hukuncin alkalan, wanda Mai Shari’a Emmanuel Agim, ya karanta, sun soki gwamnati kan yadda ta taso keyarsa daga Kenya da baruniyar hanya.

Haka kuma ta soki kotun farko da ta soke belin Nnamdi Kanu, saboda tserewar da ya yi don tsira da rayuwarsa a lokacin da sojoji suka kai hari gidansa.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...