Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dokokin Kano ta amince da mutanen da ta tattance don nada...

Majalisar dokokin Kano ta amince da mutanen da ta tattance don nada su kwamishinoni a gwamnatin Kano

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amince da kwamishinonin goma sha shida da ta tantance a ranar Laraba.

Majalisar ta amince da tantancewar ne a zaman ta na Alhamis din nan karkashin shugaban ta Jibril Isma’il Falgore.

A ranar Talata ne gwamnan Kano ya aikewa majalisar sunayen mutane 19 da yake so majalisar ta tantance don nada su kwamishinoni.

Inda a ranar Laraba majalisar ta tantance mutane 16 tare da amincewa dasu a Alhamis din nan.

Cikin mutane 19 dai akwai mutum biyu da suka tafi aikin hajji wanda hakan yasa ba a tantance su ba sai kuma mataimakin gwamnan Kano wanda aka amince dashi ba tare da ya halarci tantamcewar ba.

Shugaban masu rinjaye dan majalisa mai wakiltar Dala Lawal Hussain yayiwa wakilin mu na majalisa Aminu Abdullahi Ibrahim karin bayani.

Rashin ilimi ne yasa matasa ke aikata ta’addanci a Kano: Dan majalisar jiha mai wakiltar Bebeji Ali Muhd Tiga

Majalisa ta kuma kafa kwamiti da zai jagoranci fitar da kwamitocin majalisar na bangarori daban daban wanda shugaban majalisar zai jagoranci kwamitin.

Ga karin bayanin dan majalisa Lawal Hussain kan kwamitocin da majalisar ta fitar.

Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Aminu Abdlahi Ibrahim ya ruwaito cewa Lawal Hussain na cewa fiye da rabin aikin majalisa ya dogara ne ga kwamitoci.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...