Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar sojin ruwa ta kalubalanci ikirarin Asari Dokubo kan da sa hannun...

Rundunar sojin ruwa ta kalubalanci ikirarin Asari Dokubo kan da sa hannun su a satar man fetur

Date:

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ƙalubalanci tsohon jagoran masu fafutika na yankin Neja Delta, Mujahid Asari Dokubo da ya bayyana sunayen jami’an da ke satar ɗanyen mai.

A ranar Juma’a ne Asari Dokubo ya yi zargin cewa akwai hannun sojojin Najeriya na ruwa a yawancin laifukan satar mai da ake samu a yankin Neja-Delta.

Dokuba ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawarsa da shugaba Bola Tinubu.

Sai dai yayin da yake mayar da martani, mai magana da yawun rundunar sojin ruwan Najeriya, Commodore Adedotun Ayo-Vaughan, ya bayyana zargin a matsayin maganar da babu gaskiya a cikinta.

Ya ce ɓarayin mai sun fusata ne saboda sojojin ruwan Najeriya na ci gaba da hana su hanyoyin da za su yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta hanyar wani shiri na dakatar da ayyukan ɓarayi.

Ya ci gaba da cewa rundunar sojin ruwa tare da hadin guiwar masu ruwa da tsaki za su ci gaba da hana ɓarayin danyen mai hanyoyin yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...