Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAsari Dokubo ya zargi sojin Najeriya da satar kashi 99 cikin dari...

Asari Dokubo ya zargi sojin Najeriya da satar kashi 99 cikin dari na danyen man kasar nan

Date:

Fitaccen shugaban tsagerun yankin Neja Delta, Asari Dokubo, ya zargi sojojin Najeriya da laifin satar  kashi 99 cikin 100 na danyen mai a kasar nan.

Dokubo ya yi wannan zargin ne bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa Bola Tinubu a ofishin sa ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi alkawarin gudanar da bincike kan zargin badakalar man fetur da wasu fitattun kwamandojin ruwa wadanda suka gawurta suke gudanarwa, kuma ya yi alkawarin daukar kwararan matakai don dakatar da wannan mummunar aikin.

Dokubo ya kara da cewa, akwai wadansu jiga-jigai da ke aiki daga Abuja, yana mai shan alwashin cewa wadannan mutanen yanzu sun hadu da wanda ya fi karfin su kuma nan ba da jimawa ba za a fara tasa keyar irin waɗannan mutane zuwa gidan yari.

Ya ce za a iya amfani da yara masu yi masa aiki wurin yaki da wananan mummunar aikin.

Tsohon shugaban masu tayar da kayar bayan ya ce talakawan yankin Neja-Delta da ake zargi da satar mai ba su da ƙwarewar yin sata irin na zamani.

A cewarsa, yadda barayin man fetur ke gudanar da ayyukansu na aikata muggan laifuka, ya hana al’ummar yankin Neja-Delta gudanar da rayuwarsu, kuma hakan laifi ne na cin zarafin bil’adama.

Dokubo ya kuma yi zargin cewa wani abin kunya ne ga sojoji su ce ba su da isassun kayan yaki da za su magance matsalar tsaro, inda ya zarge su da yin watsi da makamansu ga ‘yan ta’addan, lamarin da ya ci gaba da hura wutar rikicin.

Latest stories

Related stories