Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta umarci DSS su bawa Emefiele damar ganawa da lauyoyinsa

Kotu ta umarci DSS su bawa Emefiele damar ganawa da lauyoyinsa

Date:

Kotu ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya DSS da su gaggauta bai wa gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele damar ganawa da lauyoyinsa da iyalansa ba tare da ɓata lokaci ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Umarnin ya fito ne daga mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya da ke zamanta a Maitama Abuja a ranar Juma’a.

Lauyan Emefiele JB Daudu ya sanar da kotun cewa ya rubuta wa hukumar DSS wasiku, musamman a ranar 14 ga watan Yuni domin neman ƙarin bayani daga wurinsa, amma hukumar DSS ta ƙi amsa buƙatar.

A ɗaya ɓangaren kuma lauyan waɗanda ake ƙara na biyu da na uku, I. Awo, ya shaida wa kotun cewa hukumar DSS ba ta da hurumin ƙin amincewa da wannan buƙata, kuma yin hakan ba daidai ba ne.

Sai dai ya bayyana tabbacin hukumar tsaron za ta bi umarnin kotu tare da bai wa lauyoyin da aka lissafa da kuma iyalan Emefiele damar ganin sa.

Hukumar DSS ta kama Emefiele a ranar Asabar, sa’o’i kaɗan bayan shugaba Bola Tinubu dakatar da shi daga muƙaminsa.

 

 

 

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...