Rashin ilimi ne yasa matasa ke aikata ta’addanci a Kano: Dan majalisar jiha mai wakiltar Bebeji Ali Muhd TigaDan majalisar jiha mai wakiltar Bebeji, Ali Muhammad Tiga, ya bayyana damuwar sa kan halin da ilimi ya tsinci kansa a jihar Kano.
Ali Muhd Tiga, na wannan jawabi ne yayin taron bada horo ga ‘yan majalisar dokokin Kano na majalisa ta goma.
Ya ce kasancewar sa matashi yana takaicin yadda matasa da yawa basa samun damar zuwa makaranta wanda hakan ke kara ta’azzara matsalolin rashin tsaro a jihar Kano.
Ya kara da cewa zai maida hankali wajen kawo kudororin da zasu magance matsalolin shaye shaye da wadanda zasu raya karkara.
Ali Muhammad Tiga, ya ce zai maida hankali wajen samarwa da matasan yankin Bebeji aikin yi da bada jari da samar da sana’o’in dogaro dakai.
Ya nuna farin cikin sa bisa yadda aka basu horon sanin makamar aiki kasancewar su sabbin mambobi a majalisa.