Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaban kasa Tinubu ya dakatar da Gwamnan CBN Godwin Emefiele

Shugaban kasa Tinubu ya dakatar da Gwamnan CBN Godwin Emefiele

Date:

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya dakatar da Godwin Emefiele daga shugabancin babban bankin kasa CBN.

Wannan na kunshe a wata sanarwa da darakta a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey ya fitar a daren jiya Juma’a.

Sanarwar ta alakanta daukar matakin da binciken dake wanzuwa kan yadda Emefielen ya tafi da wasu al’amuran babban bankin.

Tuni dai aka maye gurbinsa da mataimakinsa na sashin ayyuka, wato Folashodun Adebisi.

Tun a baya dai, shugaba Tinubu yayi zargin cewa shirin sauya fasalin kudi da aka bijiro da shi babu zato, karkashin Emefiele, an yi hakan ne da gan gan, domin haifar masa da cikas wajen samun nasara a zabe.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...