Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar Sojin Najeriya Ta Tabbatar Da Mutuwar Tarin Dakarunta Da Yan Ta'addan...

Rundunar Sojin Najeriya Ta Tabbatar Da Mutuwar Tarin Dakarunta Da Yan Ta’addan Boko Haram Suka Kaiwa Hari A Yankin Tafkin Chadi

Date:

Rundunar sojin kasar nan ta tabbatar da mutuwar tarin dakarunta yayin wani hari da yan ta’addan Boko Haram da ke biyayya ga kungiyar IS suka kai musu a yankin tafkin Chadi.

Rahotanni sun ce mayakan ISWAP ne suka kai wa ayarin dakarun hari a kauyen Metele na jihar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata lamarin da ya kai ga ba-ta-kashi, inda daya daga cikin ‘yan ta’addan ya tayar da damarar bam din da ke jikinsa.

Majiyoyin sojin sun ce sun yi asarar dakarunsu da dama, amma ba za su iya fadin adadin wadanda suka kwanta daman ba.

Rahotanni sun ce ayarin sojojin na kan hanyarsa ta zuwa garin Arege, wanda ke kan iyakar kasar nan da Nijar da Chadi don kai wa dakarun da su ke yaki da ‘yan ta’adda yankin abinci ne suka gamu da wannan harin.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet da ake kira SITE, kungiyar ISWAP ta ce lallai ita ta kai wannan harin, kuma bam din da ya tarwatse ya lalata wasu motocin soji masu sulke guda biyu.

ISWAP ta kuma yi ikirarin karbe dimbim makamai daga ayarin sojojin.

RFI

Latest stories

Related stories