Saurari premier Radio
33.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRuwan Sama Da Iska Sun Kashe Mutane Biyu Tare Da Rushe Gidaje...

Ruwan Sama Da Iska Sun Kashe Mutane Biyu Tare Da Rushe Gidaje Sama Da 20 A Jihar Jigawa

Date:

Ruwan sama da iska mai karfi sun yi sadiyar mutuwar mutane biyu da kuma jikkata wasu da dama tare da rushe gidaje sama da 20 a garuruwan Larabawa da Hambarawa da ke yankin karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban karamar hukumar, Alhaji Shehu Sule Udi, ya ce al’amari ya faru da misali karfe  daya na daren ranar Litinin bayan tasowar hadari da iska mai karfi.

Ya ce iftila’in da ya shafi garuruwan Larabawa da Hambarawa, ya janyo asarar rayuka da jin munanan raunuka da kuma rushewar gidaje.

Alhaji Shehu Udi ya ce karamar hukumar za ta tallafawa wadanda iftila’in ya shafa domin rage musu radadin halin da suka shiga.

A bangaren su mutanen da iftila’in ya shafa sun bukaci gwamnati da ta kawo musu daukin gaggawa.

Latest stories

Related stories