Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Thursday, May 16, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKarfafar Kananan Masana'antu Ne Ke Habbaka Tattalin Arziki - Mai Dakin Gwamnan...

Karfafar Kananan Masana’antu Ne Ke Habbaka Tattalin Arziki – Mai Dakin Gwamnan Lagos.

Date:

Mai dakin gwamnan gwamnan jihar Lagos, Dr. Ibijoke Sanwo-Olu, ta jaddada kudirin gwamnatin mai gidanta na karfafawa tare da tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da matasa da matasa da kuma masu bukata ta musamman wajen cigaban su.

Yayin taron baje koli da nune-nune na Yello Care, wanda ya gudana a jihar Lagos, Dr. Ibijoke ta bayyana muhimmancin kanana da matsakaitan masana’antu a matsayin abinda ke haddaka tattalin arziki.

Ta yi kira ga manyan kamfanoni da su hada hannu da gwamnatin jihar ta Lagos wajen karfafar kanana da matsakaitun masana’antu don ganin cigaban su.

Wakilinmu da ke jihar ta Lagos, Abdulrasheed Hussain ya rawaito cewa, yayin taron da ya gudana a babban ofishin kamfanin sadarwa na MTN, an kaddamar da wani shiri mai suna, Yello Den-Pitch-A-Thon, da hadin gwiwar bankin masana’antu, in da masu sana’oi da suka cancanta za su samun tallafin kudi daga kamfanin MTN, wanda za su fadada kasuwancinsu.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...