Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAmbaliyar ruwa ta shafe sama da gidaje 100 a Abuja

Ambaliyar ruwa ta shafe sama da gidaje 100 a Abuja

Date:

Rahotanni daga yankin birnin tarayya sun ce fiye da gidaje dari ambaliyar ruwa ta shafa a rukunin gidajen Trademore da ke unguwar Lugbe a Abuja.

Wannan ya biyo bayan mamakon ruwan sama da iska da aka tafka jiya Juma’a, wanda kuma ya yi sanadin asarar kayayyaki masu darajar milyoyin naira.

Babban daraktan hukumar agajin gaggawa ta birnin tarayya, Dr Abbas Idris da ya tabbatar da haka a wata sanarwa, ya ce an ceto kusan mutane hudu da ruwan ya kusa yin awon gaba da su.

Wasu hotunan bidiyo sun nuna mazauna unguwar na fafutukar neman tsira da rayukansu, yayin da kuma wasu ke kokarin tsintar kayayyakin amfani.

Wannan ba shi ne karon farko da unguwar Lugbe ta fuskanci ambaliyar ruwa ba a ‘yan shekarun nan.

 

Latest stories

Related stories