Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu bai yanke hukunci na karshe kan makomarsa ta siyasa ba, duk kuwa da rade-radin da ake yadawa kan cewar akwai yiwuwar sauya sheka daga jam’iyyar ADC.
A wata sanarwa da ya fitar, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ce akwai bayanai masu rudani da ke yawo a kafafen yada labarai, dangane da matsayinsa a siyasa, musamman yadda rikicin shugabanci ya addabi jam’iyyar ta ADC.
Ya bayyana cewa hukuncin kotun koli da ya tabbatar da halascin kwamitin gudanarwa na kasa, karkashin jagorancin Sanata David Mark ya kuma mayar da shari’ar zuwa kotun kasa, lamarin da ya sanya jam’iyyar cikin wani yanayi mai sarkakiya.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kara da cewa, wata babbar kotun tarayya ta kuma soke halascin babban taron jam’iyyar na baya-bayan nan, yayin da babban lauyan gwamnatin tarayya ya nemi wata kotu ta soke rajistar jam’iyyar ta ADC.
Saboda haka, ya ce shi da sauran masu ruwa da tsaki sun fara tuntubar wasu jam’iyyu da shugabanninsu ciki har da NDC da PRP domin daukar mataki na gaba.
